Yan bindiga sun sace ɗaliban firamare a Kaduna
Yan bindiga sun sace ɗaliban firamare a Kaduna
![Labari da dumi-dumi](https://ichef.bbci.co.uk/news/640/cpsprodpb/1638E/production/_97722019_de89dee6-a373-4371-8c58-a9d3791f8291.jpg)
Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗaliban firamare da malamansu a ranar Litinin.
An sace ɗaliban ne a makarantar firamare ta Rema da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa.
Wani jami'in gwamnati ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun kutsa kai cikin wani aji, inda suka yi awon gaba da yara biyu da malamansu biyu.
Comments
Post a Comment