Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin dan adam Author: Abubakar Nura Bal a Kankana tana da matukar mahimmacin kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda ‘ya’yanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus da copper. ‘yayan kankana wadan da ake kira da ‘tarbooj ke beeja’ yaren hindi, ana amfani dasu kamar a kasar Asia, a matsayi kayan abinci, inda a Najeriya kuma ake amfani da ita a cikin miya, inda man ‘ya’yan kuma ana amfani dashi a don gyara fatar jiki. Ga wasu daga cikin amfanonin ‘ya’yan kankana a jikin dan adam: 1. ‘Ya’yan kankana suna water da jikin dan adam da sinadaran magnesium wanda ke taimakawa zuciya wurin harba jinni da kuma magance ciwon diabetis. 2 .‘Ya’yan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji. 3. ‘Ya’yan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jiki lafiyar jinin dan a...